Ma Zhaoxu, ya bayyana hakan ne, yayin bude mahawarar kwamitin tsaron MDD game da hadin gwiwar majalissar da sauran sassan yankunan duniya, yana mai fatan irin wannan hadin gwiwa, zai haifar da kyakkyawar dama, ta shawo kan kalubalen dake addabar yankunan bisa yanayin su.
Ya ce hukumomin yankuna, da na sassa daban daban, na da masaniyar tarihin su, da al'adun su, da ainihin halin da suke ciki. Suna kuma da dama ta zakulo dabaru mafiya dacewa na magance matsalolin su, sabanin duk wata hanya da ta sabawa hakan. (Saminu Alhassan)