in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Cin hanci da rashawa ya haddasa hasarar kashi 5 bisa 100 na GDPn duniya
2018-12-06 10:51:47 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya sanar a jiya Laraba cewa rashawa ta yi sanadiyyar tafka hasarar kimanin dala trillion 2.6, kwatankwacin kashi 5 bisa 100 na kudaden shiga na (GDP) na duniya baki daya.

Kaucewa biyan haraji, yin sama da fadi da kudade, da sauran ayyukan da suka shafi zambar kudi ko kuma karkata akalar kudade da ake bukatarsu wajen gina dauwwamamman ci gaba, kamar yadda bankin duniya ya bayyana, da harkokin cinikayya tsakanin mutane inda ake biyan sama da dala trillion 1 a matsayin cin hanci a duk shekara, in ji babban jami'in MDD a sakon da ya gabatar domin ranar da MDD ta ware ta kasa da kasa don yaki da rashawa, wanda za'a gudanar a ranar 9 ga watan Disamba.

Guterres ya ce rashawa, "tana rusa makarantun ilmi na al'umma, da asibitoci, da sauran muhimman fannonin rayuwar al'umma, tana lalata jarin kai tsaye na kasashen waje, da kuma lalata albarkatun kasashen duniya," da kawo koma baya ga tsarin doka da oda, da haddasa yawaitar muggan laifuka a tsakanin jama'a, kamar safarar bil adama ta haramtattun hanyoyi, da fataucin miyagun kwayoyi da na makamai da dai sauransu.

"Rashawa tana kara haifar da rashawa da haddasa aikata ba daidai ba a tsakanin alumma," in ji mista Guterres.

"Amfani da ranar da MDD ta kebe don yaki da rashawa na daga cikin muhimman hanyoyin da muke amfani da su wajen karfafa yaki da rashawa" in ji jami'in MDD, ya kara da cewa, ta hanyar wannan rana za mu sake bibiyar karin matakai da suka dace mu dauka don cimma wannnan buri. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China