Madam Lagarde ta yi wannan kira ne a jiya Talata, yayin da take jawabi a dakin karatu na majalisar dokokin Amurka dake birnin Washington D.C. Jawabin uwargida Lagarde shi ne na baya-bayan a jerin laccocin Kissinger da ake gabatarwa sau biyu a shekara, inda ake gabatar da manufofin ketare da alakar kasashen duniya.
Shugabar ta kuma shawarci kasashe masu karfin tattalin arziki da su karfafa hadin kai a manyan fannoni hudu da suka hada cinikayya da harajin kasa da kasa da sauyin yanayi da yaki da cin hanci da rashawa.(Ibrahim)