in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF: karin kudin fito zai yiwa GDPn duniya illa
2018-07-23 10:18:20 cri

Babbar darektar hukumar bayar da lamuni ta duniya ko IMF a takaice Christine Lagarde ta sake nanata yadda manufofin ba da kariya ga harkokin cinikayya za su yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya.

Lagarde wadda ta bayyana hakan ranar Asabar din da ta gabata yayin taron manema labarai a Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina, ta kuma lura da hasashen baya-bayan da aka yi game da alkaluman GDPn duniya biyo bayan karin kudin fito da Amurka ta sanyawa wasu hajojin da aka shigarwa cikin kasar daga ketare

Jami'ar ta ce asusun na IMF ya auna irin mummunan tasirin da kariyar cinikayyar da za ta haifar, sakamakon karin harajin. A cewarta hakan zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin Amurka gami da alkaluman GDP na duniya baki daya.

A baya-bayan nan asusun na IMF ya yi hasashen cewa, idan har aka aiwatar da harajin da ake barazanar sakawa, to ci gaban GDP na duniya zai ragu da kaso 0.5 cikin 100 nan da shekarar 2020.

Babbar darektar ta IMF ta je birnin Buenos Aires ne don halartar taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kasashen G20.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China