Cikin sabon rahoton hasashen tattalin arzikin duniya da ya fitar jiya Litinin, IMF ya ce tattalin arzikin duniya zai kai kaso 3.9 a shekarar 2018 da ta 2019, kamar dai yadda ya fada a watan Afrilun da ya gabata.
Sai dai ba ko ina ne ci gaban tattalin arziki za ta shafa ba, kuma hadduran dake tattare da ita na karuwa. Sannan ci gaban ya kai matsayin koli a wasu kasashen. (Fa'iza Mustapha)