Abebe Selassie, ya ce hadin gwiwar Sin da Afrika, bai tsaya a fannin harkar kudi ba, domin hadin gwiwa ce da ta kunshi fannoni da dama.
Yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan, ya ce a ganinsa, kasar Sin muhimmiyar kwarin gwiwa ce ga kasashe masu tasowa da kuma kasashen Afrika, wadda ta ke nuna cewa za kasa za ta iya samun ci gaba cikin sauri cikin wani lokaci, tare da tashi daga kasa mai talauci zuwa mai samun matsakaicin kudin shiga.
Ya kara da cewa, kasar Sin muhimmiyar abokiyar hulda ce a fannin cinikayya da ci gaba ga nahiyar, kuma akwai ilimi mai tarin yawa da nahiyar ta samu daga kasar Sin, ya na mai cewa bai dace a kalli hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuska guda ba.
Ya ce taron FOCAC da za a yi yau da gobe, na zuwa ne a wani muhimmin lokaci da ake sa ran kasar Sin za ta tabbatar da kudurinta da goyon baya ga ci gaban nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)