Kwanan baya, wasu kafofin yada labarai na yammacin kasashen duniya sun yi zargin cewa, ayyukan gina ababen more rayuwa da kasar Sin ta yi a kasashen Afirka, za su kawo wa kasashen Afirka babbar matsala ta bashi. Dangane da wannan lamari, Mr. Selassie ya ce, a halin yanzu, kasashen Afirka guda 6 zuwa 7 ne kadai suke fama da matsalar bashi, ko kuma suke fuskantar babban kalubale na shiga cikin wannan matsala, kuma sun samu rancen kudadensu ne daga kasashe daban daban, ba wai kasar Sin ita kadai ba.
Ya kara da cewa, jarin da kasar Sin ta zubawa kasashen Afirka, ba kawai domin su biya bukatun kasashen Afirka ba ne, har ma ana fatan za su samar wa kasashen babbar moriya. Ana da imanin cewa, kasashen Afirka za su iya neman dauwamammen ci gaba, da kuma rage kalubalen bashinsu, bisa jarin da kasar Sin ta samar musu, da kuma karin hajojin da za su fitar zuwa kasar ta Sin. (Maryam)