in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun tsaron Afrika sun fara shirin samun horon soji a gabashin Uganda
2018-08-31 09:40:45 cri
Sama da dakarun tsaron kasashen Afrika 350 ne suka shiga wani shirin samun horo na sojoji na tsawon mako guda domin sanin makamar aiki ta yadda za su tinkari matsalolin tsaro a nahiyar.

Laftanal kanal Deo Akiiki, mataimakin kakakin rundunar sojojin Uganda ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, shirin bada horon na aikin sa kai karkashin shirin kai daukin gaggawa yayin barkewar rikici na Afrika wato (ACIRC), an tsara shirin ne da nufin samarwa dakarun tsaron kwarewar aiki ta yadda za su yi aiki tare don tabbatar da tsaro da ba da kariya.

Laftanal Janar Wilson Mbadi, mataimakin babban hafsan rundunar tsaron Uganda, shi ne ya jagoranci bude shirin wanda aka yiwa lakabin "UTULIVU AFRICA IV" ya ja hankalin dakarun tsaro daga kasashen Algeria, Angola, Burkina Faso, Benin, Chad, Masar, Niger, Rwanda, Senegal, Tanzania, Afrika ta kudu, Sudan da kuma Uganda.

Wata sanarwar da hukumar sojojin ta fitar ta ce, dakarun tsaron za su hallara ne a cibiyar ba da horo ta Uganda, dake gabashin garin Jinja.

Mbadi ya ce kasashen Afrika ne suka tsara shirin da nufin warware matsalolinsu da kansu da kuma rage yin shisshigin da kasashen waje ke yi wa harkokin cikin gidan nahiyar.

Maj. Gen. Mark Nakibus Lakara, daraktan shirin, ya ce shirin bada horon zai taimakawa dakarun tsaron na ACIRC a nan gaba ta yadda za su iya samun damar gudanar da ayyukan da suka shafi kai dauki gaggawa wanda ya dace da dokokin kungiyar tarayyar Afrika AU.

Sivuyille Bam, wanda ya wakilci kungiyar AU, ya yabawa hukumar gudanarwar shiyyar sakamakon bullo da shirin wanda zai taimakawa dakarun tsaron Afrika a daidai lokacin da ake da bukatar hakan a yayin da AU da MDD suke ta kokarin yin aiki tare wajen samar da kayayyakin da ake bukata domin tura dakarun wanzar da tsaro a sassan nahiyar da ake fama da rikice rikice. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China