in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin-gwiwar Sin da Afirka na bayar da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban Afirka
2018-12-04 20:09:50 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana yau Talata a birnin Beijing cewa, ana kara samun kwararan shaidun dake nuna cewa, hadin-gwiwar da kasar Sin ke yi da kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka, na samar da babban taimako da muhimmiyar gudummawa ga bunkasuwar tattalin arziki da kyautatuwar rayuwar al'umma a wurin.

Rahotanni sun ruwaito cewa, a kwanakin baya, gidan rediyon NPR na kasar Amurka ya gabatar da wani sabon rahoton bincike da kwalejin William & Mary ta kasar ta bayar, inda aka nuna cewa, muhimman ababen more rayuwar jama'ar da kasar Sin ta gina a wasu kasashen Afirka na kara haskaka kasashen, da kuma samar musu da kyakkyawar makoma. Haka kuma rahoton ya ce, muhimman ababen more rayuwar al'umma da kasar Sin ta gina a wasu kasashe dake tasowa, musamman kasashen Afirka, sun taimaka sosai ga habakar tattalin arzikin wurin.

Geng Shuang ya nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada kai tare da kasashen Afirka, don tabbatar da daukar wasu muhimman matakai takwas na inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka da shugaba Xi Jinping ya sanar a wajen taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC wanda aka yi a Beijing. Haka kuma Sin na son kara hada kai tare da sauran kasashen duniya don taimakawa kasashen Afirka wajen shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China