Kasar Sin za ta ware kason kudi na dala biliyan goma don raya Sin da Afirka da kafa gamayyar bankunan Sin da Afirka
Jaridar Economic Daily ta kasar Sin ta ruwaito cewa, babban masanin ilmin tattalin arzikin bankin raya kasar Sin, Liu Yong ya bayyana a jiya Alhamis cewa, bankin raya kasa wato bankin CDB zai dauki wasu muhimman matakai a fannoni da dama don goyon-bayan karfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ciki har da bunkasa masana'antu, da hade ababen more rayuwa, da saukaka matakan cinikayya, da neman bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da inganta kwarewa da kara mu'amalar al'adu da sauransu.
Matakan da bankin zai dauka sun hada da, na farko, ware wani kason kudi na musamman da ya kai dala biliyan goma don raya harkokin Sin da Afirka. Na biyu, kafa gamayyar bankunan Sin da Afirka don karfafa hadin-gwiwar bangarorin biyu a fannin harkokin kudi. Na uku kuma, rattaba hannu kan yarjeniyoyin samar da rancen kudi da dama.(Murtala Zhang)