in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya dandalin tattaunawa kan harkokin kasuwanci na Sin da Afirka a Beijing
2018-05-24 20:55:56 cri

Gabannin "Ranar Afirka" karo na 55, domin taya kungiyar tarayyar Afirka wato AU murnar cika shekaru 55 da kafuwa, tawagar jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin gami da cibiyar musanyar al'adu da harkokin diflomasiyya ta kasar sun shirya taron dandalin tattaunawa kan harkokin kasuwanci na Sin da Afirka na shekara ta 2018 a yau Alhamis a birnin Beijing. Wakilan jami'an diflomasiyyar Afirka dake kasar Sin da wakilan MDD, gami da Sinawa daga bangarorin masana'antu da kafofin watsa labarai da ilimi sama da 350 ne suka halarci taron.

A jawabinsa yayin taron jakadan kasar Rwanda a kasar Sin, Charles Kayonga ya bayyana cewa, taron yau zai taimaka wajen hada kan kasashen Afirka da kamfanonin kasar Sin, da kyautata yanayin zuba jari na kasashen Afirka, da taimakawa kamfanonin kasar Sin su je Afirka su zuba jari.

A nasa bangare, shugaban cibiyar musanyar al'adu da harkokin diflomasiyya ta kasar Sin, Ma Zhenxuan, ya ce yana fatan taron na yau zai kara fahimtar juna tsakanin kamfanonin kasar Sin da kasashen Afirka, da karfafa zumunci tsakanin al'ummominsu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China