Masana dokokin Afirka na sa ran hadin-gwiwar Sin da Afirka za ta samar da sabon zarafi ga ci gaban Afirka
Yau Laraba, a birnin Beijing na kasar Sin, aka rufe dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasashen duniya ta fuskar doka bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya' da ma'aikatar harkokin wajen Sin da kungiyar masana dokoki ta kasar suka shirya.
A yayin dandalin tattaunawar, an bayar da sanarwar shugaba ta hadin-gwiwa, inda masana dokoki daga kasashen Afirka ke sa ran cewa, hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar doka bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya' za ta samar da sabon zarafi ga ci gaban nahiyar Afirka baki daya.(Murtala Zhang)