A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, 'yan kasuwa na kasashen biyu, sun taka muhimmiyar rawa wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, don haka ya kamata kasashen biyu sun rike damarsu, da yin kokarin fadada hadin gwiwarsu. Ya ce Sin ta bude kofa ga kasa da kasa cikin sahihanci, da yin maraba da 'yan kasuwa daga kasa da kasa, ciki har da kasar Panama a fannin zuba jari da kafa kamfanoni a kasar Sin, da kuma sa kaimi ga kamfanonin Sin, wajen fadada ayyukansu a kasar Panama, don samun bunkasuwa da wadata tare.
A nasa bangare, shugaba Varela ya yi maraba da kamfanonin Sin da su shiga kasuwannin kasarsa domin zuba jari, da maida kasar Panama a matsayin muhimmin wurin fadada ayyukansu a nahiyar Latin Amurka, da taimakawa kasar wajen samun ci gaba, da cimma burin samun moriyar juna ta hanyar hadin gwiwar da shugaba Xi Jinping ya gabatar. (Zainab)