in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Panama sun amince da kara zurfafa dangantaka
2018-12-04 09:48:14 cri

A jiya Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Panama Juan Carlos Varela, suka cimma matsaya game da kara zurfafa dangantakar kasashen su.

Shugaba Xi ya isa Panama ne a ranar Lahadi, ziyara irinta ta farko da wani shugaban kasar Sin ya kai kasar dake nahiyar tsakiyar Amurka, tun bayan kulla hulda tsakanin sassan biyu a shekarar 2017.

Da yake tsokaci, shugaban na Sin ya jinjinawa tasirin dangantakar kasarsa da Panama, wanda ya haifar da nasarori da dama ciki hadda musayar al'umma masu ziyarar kasashen juna, da ziyarar shugabannin kasashen, da kuma zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa.

Shugaba Xi ya ce a zahiri take cewa, kulla huldar diflomasiyya ita ce hanya mafi dacewa wadda za ta ci gaba da amfanar al'ummun kasashen biyu. Kaza lika Sin za ta ci gaba da tallafawa kokarin Panama na inganta tsaron kasa, da samar da daidaito, da kyautata rayuwar al'umma, da habaka tasirinta a harkokin kasa da kasa, baya ga fadada rawar da kasar za ta ci gaba da takawa a fannin inganta tattalin arzikin shiyyar, tare da hadewarta da sauran kasashen duniya.

Yayin da suke zantawa, shugabannin biyu sun tabo batu game da irin ci gaba da aka samu, da kuma ingantar hadin gwiwar dake tsakani tun bayan kulla kawancen kasashen biyu. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China