in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya nuna yabo kan yadda aka cimma daidaito wajen taron G20
2018-12-03 13:44:14 cri
Sakataren janar na MDD Antonio Guterres, ya sanar a jiya Lahadi cewa, yana farin ciki kan yadda shugabannin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20, suka cimma daidaito kan batutuwan da suka hada da ra'ayin sanya bangarori daban daban su shiga a dama da su, da yunkurin neman ci gaba mai dorewa, da aikin tinkarar sauyawar yanayin duniya, da dai makamantansu.

A cewar mista Guterres, sanarwar da aka gabatar a karshen taron G20, ta shaida yadda shugabannin kasashe mambobin G20 suka lura da muhimmanci na yin amfani da manufar da ta kunshi ra'ayoyin bangarori daban daban wajen daidaita al'amura a fannin ciniki, gami da yin kwaskwarima kan kungiyar ciniki ta duniya WTO.

Haka zalika shugabannin sun nanata alkawarinsu na ci gaba da bin tsarin duniya da aka kafa bisa ka'idojin kasa da kasa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China