in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron G20 ya amince da tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa da yi wa tsarin WTO garambawul
2018-12-02 16:16:05 cri
An kammala taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20 jiya Asabar a birnin Buenos Aires, inda mambobinta suka bayyana amincewarsu da tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa, tare da yin kira da yi wa tsarin hukumar kula da harkokin cinikayya ta duniya WTO garambawul.

Sanarwar karshe da taron ya fitar, ta ce mambobin kungiyar sun bayyana cewa, cinikayya da zuba jari tsakanin kasa da kasa muhimman abubuwa ne dake haifar da ci gaba da samar da aikin yi da kirkire-kirkire. Kuma sun lura da irin gudunmuwar da tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa ya bayar ga wadancan abubuwa.

Sai dai sun ce a yanzu, tsarin baya cimma burinsa kuma akwai damarmakin inganta shi. A don haka, suke mara baya ga yi wa WTO garambawul din da take bukata domin inganta ayyukanta, suna masu cewa za su yi bitar nasarorin da za a samu a wannan fanni yayin taronsu na gaba.

A game da batun sauyin yanayi kuwa, sanarwar ta ce wadanda suka cimma yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris, sun jadadda cewa babu batun komawa baya dangane da yarjejeniyar kuma sun kuduri niyyar aiwatar da kunshinta, wanda ke nuna buri na bai daya da suke da shi mai kunshe da hakkoki da karfi mabanbanta.

Taron na yini 2 mai taken 'cimma daidato don samun ci gaba mai dorewa' ya tattauna akan batutuwan da suka shafi makomar ayyuka da raya ababen more rayuwa da daidaituwar harkokin kudi da sauyin yanayi da cinikayya tsakanin kasa da kasa da dai sauransu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China