Jakadan Sin: Ana fatan ganawar da za a yi tsakanin shugabannin Sin da Amurka za ta tabbatar da makomar hulda tsakanin kasashen 2
Cui Tiankai, jakadan kasar Sin a kasar Amurka, ya furta yayin da yake hira da manema labaru a yau a birnin Washington cewa, ana fatan ganawar da shugaban kasar Sin zai yi da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump za ta tabbatar da makomar huldar dake tsakanin kasashen 2, musamman ma a fannin daidaita wasu matsaloli, ciki har da batun da ya shafi tattalin arziki da cinikayya.
Jakadan ya ce, shugabannin kasashen 2 za su gana da juna yayin taron kungiyar G20 da za a kaddamar a ranar 30 ga watan da muke ciki a kasar Argentina. Saboda haka, bangarorin Sin da Amurka suna kokarin share fage don neman tabbatar da ganin an gudanar da ganawar lami lafiya. (Bello Wang)