in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Botswana ya bukaci a kara kokarin fatattakar cutar kanjamau
2018-12-02 16:25:48 cri
Shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, ya yi kira da a kara kaimi ga kokarin fatattakar cutar kanjamau.

A jawabin da ya gabatar domin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya na bana a kauyen Mochudi dake da nisan kilomita 60 daga wajen birnin Gabarone, Mokgweetsi Masisi ya ce yarda da kai ya sa ana mayar da hannun agogo baya dangane da nasarorin da aka samu na yaki da cutar kanjamau.

An yi kiyasin yawan masu cutar a Botswana ya kai kashi 18.5 cikin 100, inda kasar ke matsayi na 3 a yankin kudancin Afrika bayan Swaziland da Lesotho.

Ya ce alama daya da za ta nuna cewa kasar ta dauki kyakkyawar alkibla shi ne, lokacin da babu sabon rahoton kamuwa da cutar.

A don haka, shugaba Masisi ya bukaci al'ummar kasar su yi nazari tare da shiga cikin yaki da cutar ta yadda kasar za ta fatattake ta baki daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China