in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda na shirin kawar da kyamar da ake nuna wa masu dauke da cutar kanjamau nan zuwa 2020
2017-03-03 10:37:22 cri

Gwamnatin Rwanda ta jaddada kudurinta na kawo karshen kyamar da ake nunawa masu dauke da cutar kanjamau nan zuwa shekarar 2020

Da yake ganawa da manema labarai jiya Alhamis, darakta a ma'aikatar kula da lafiya ta kasar Ribarakare Mpundu ya ce, kyamar da ake nunawa masu dauke da cutar kanjamau na ci gaba da jefa su cikin hadari, inda yake sa wasu boye cutar, tare da kin zuwa karbar shawarwari da kuma magunguna.

Ya ce, daga nan zuwa shekarar 2020, an shirya gudanar da gangamin wayar da kan jama'a, da nufin kawo karshen nuna kyama, da kuma ba da damar zuwa agaji kyauta da karbar shawarwari da magunguna.

Ya ce, sun yi imanin cewa, idan duka masu cutar za su yi amfani da shawarwarin da ake ba su, tare da shan magaunguna yadda ya kamata, to babu wanda zai rasa ransa sanadiyyar cutar.

Wata kididdigar da ma'aikatar ta yi, ta bayyana cewa, a ko wace shekara a kalla mutane 10,000 ne ke kamuwa da cutar, kuma kimanin mutanen da suka kamu da ita 80, 200 na karbar magunguna.

Ma'aikatar ta kara da cewa, ana ganin tasirin magugunan da ake dora masu cutar a kai, kan kimanin kashi 81 cikin dari na masu cutar kanjamau.

A bara ne gwamnatin Rwanda, ta kaddamar da wani shiri mai suna 'Treat All' dake da nufin kula da ba da magani ga duk wanda ya kamu da cutar kanjamau, tare da kawar da duk wani nau'i na kyama da ake nuna musu.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China