in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta daura damarar dakile yaduwar kwayar cutar HIV
2017-06-21 09:06:00 cri

Gwamnatin Nijeriya ta ce, tana shirin aiwatar da wasu sabbin dabarun yaki da cutar HIV, da kuma kula da masu dauke da ita, inda za a hade su da matakan da aka dauka a baya na dakile cutar.

Ministan lafiya na kasar Isaac Adewole ne ya bayyana haka, yayin wani taro da ya gudana jiya a jihar Kaduna dake arewacin kasar, inda ya ce, a karkashin sabbin dabarun, za a rika kula da ba da magani kyauta ga wadanda ke dauke da cutar a dukkan matakai a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu.

Ya ce, daga ranar, duk wani mai dauke da cutar ko mace ko namiji, ko yaro ko mace mai juna biyu, ya cancanci samun kulawa kyauta, sannan, duk wadanda ke karbar magani, za su rika samun gwajin matakin cutar a cikin jininsu a kalla sau daya a shekara.

Ministan ya bukaci gwamnatocin jihohin kasar da sauran masu ruwa da tsaki su aiwatar da kunshin dabarun yadda ya kamata domin murkushe yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China