in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na'urorin tsaron sararin saman Syria sun kakkabo makamai masu linzami da ake zargin Isra'ila da harbawa kasar
2018-11-30 10:57:52 cri

Na'urorin tsaron saman Syria, sun kakkabo wasu makamai masu linzami da ake zargin Isra'ila da harbawa kan sansanonin soji dake yankunan kudancin kasar a jiya Alhamis.

Rahoton Gidan talabijin na Syria, ya ruwaito cewa, a wani mataki na mayar da martani, sojojin saman kasar sun harba na'urorin kakkabo makamai masu linzami, yana mai cewa an kakkabo dukkan makaman, inda harin ya gaza cimma manufarsa.

Rahoton ya kara da cewa, an kai harin ne kan garin Kisweh dake kudancin birnin Damacus.

Yayin da kafofin yada labarai na Syria ke dora alhakin harin a kan Isra'ila, ita ma kungiyar kare hakkokin bil adama ta Syria, wadda ke da mazauni a Birtaniya, ta bayyana cewa Isra'ila ce ta kai harin a yankunan kudu da kudu maso yammacin wajen birnin Damascus, kusa da iyakar lardin Quneitra dake kudancin kasar.

Kungiyar ta ce sojin saman Syria sun harba na'urorin kakkabo makaman na Isra'ila. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China