in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan gudun hijirar Syria 100,000 dake Lebanon za su koma gida zuwa karshen shekara
2018-10-10 10:57:46 cri
Shugaban hukumar tsaron kasar Lebanon Abbas Ibrahim, ya ce adadin 'yan gudun hijirar Syria da za su koma gida ya zuwa karshen shekarar nan ya kai 100,000.

Jaridar Elnashra mai wallafa labaranta a intanet, ta ruwaito Abbas Ibrahim na cewa, hukumar na bada tsaro da mafaka, baya ga yafiyar haraji ga 'yan gudun hijirar dake zaune a kasar ba bisa ka'ida ba, domin gaggauta komawarsu gida.

Ya ce hukumomin tsaron Lebanon na aiki da hukumar MDD mai kula da 'yan gudun hijira domin tabbatar da mutane sun koma gida lafiya, kuma bisa radin kansu.

Ya kuma yabawa yunkurin hukumomin Rasha dangane da aikin.

Domin mayar da 'yan gudun hijirar kasarsu, Rasha ta gabatar da wani kuduri ga hukumomin tsaron Lebanon, wanda ke da nufin tabbatar da komawar 'yan gudun hijira 890,000 zuwa Syria. (Fa'iza Muistapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China