in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar luguden wutan dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta sun kashe fararen hula 40 a gabashin Syria
2018-11-18 16:31:34 cri

A kalla fararen hula 40 ne suka mutu da safiyar jiya Asabar, sanadiyyar karuwar luguden wutan da dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta ke yi a gabashin Syria.

Kamfanin dillancin labarai na SANA na Syria, ya ruwaito cewa, an yi luguden wutan ne kan kauyen al-Bukan dake kusa da garin Hajin, mai tazarar kilomita 110 daga kudu maso gabashin lardin Deir al-Zour na gabashin Syria.

Harin wani bangare ne na hare-hare ta sama da ake kai wa wuri na karshe dake karkashin ikon mayakan IS a gabashin lardin Deir al-Zour.

Kamfanin dillancin labarai na SANA ya ce kauyen Bukan ya zama tamkar kango saboda yadda mutane ke tserewa hare-haren jiragen Amurka, wadanda ake kai wa da nufin lalata duk wani abu mai amfani ga mayakan IS

Cikin makon da ya gabata, hare haren sun yi sanadin mutuwar fararen hula sama da 100.

Ita ma kungiyar dake rajin kare hakkin dan Adam ta kasar, ta ce hare-haren dakarun kawancen sun kashe fararen hula 43 a jiya, ciki har da yara da mata 29.

Kungiyar ta ce adadin wadanda suka mutu shi ne mafi yawa a gabashin gabar kogin Eupharate dake gabashin Deir al-Zour, tun bayan da ayyukan dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta ya fara cikin makonni 10 da suka shude.

Luguden wuta da dakarun ke kai wa wuri na karshe dake karkashin IS a gabashin gabar Kogin Eupharate ya karu a baya bayan nan, inda mayakan kurdawa da Amurka ke marawa baya ke shirya wani farmaki na biyu kan mayakan IS, bayan wanda suka gaza cimmawa a watan Satumba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China