in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Syria ya tattauna batun kafa kwamitin tsara kundin mulkin kasa da jakadan Rasha
2018-11-05 11:44:18 cri

Shugaba Bashar al-Assad na Syria, ya tattauna batun kafa kwamitin tsara kundin mulkin kasarsa, da jakadan musamman na shugaban Rasha Alexander Lavrentiev, wanda ke ziyarar aiki a kasar.

Ziyarar Mr. Lavrentiev ta zo ne 'yan kwanaki, bayan da wakilan kasashen Rasha, da Turkiyya, da Jamus, da Faransa suka gudanar da taro a birnin Santambul na kasar Turkiyya game da shirin kafa kwamitin.

Wani rahoto ya nuna cewa, mahukuntan Syria da na Rasha, sun amince su ci gaba da aiki tare, domin kawar da duk wani tarnaki, da kafa sahihin kwamiti, wanda zai tsara kundin mulkin kasar bisa doka. Da ma dai shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya taba bayyana fatan sa na ganin wannan kwamiti ya fara aiki, kafin karshen wannan shekara ta 2018.

Kwamitin tsarin mulkin na kunshe da mambobi 150, wadanda aka raba su daidai tsakanin sassa 3, wato bangaren gwamnati, da na 'yan adawa, da kuma tsagin Staffan de Mistura, wakilin MDD game da batun kasar ta Syria.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China