in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake bude ma'adanar kayayyakin tarihi ta kasar Syria
2018-10-29 12:24:24 cri

Bayan shafe tsawon shekaru 6 da rufe wajen, sakamakon dalilai na tsaro, an sake bude ma'adanar kayayyakin tarihi ta kasar Syria a jiya Lahadi.

Wasu jami'an gwamnatin kasar Syria, da masana masu nazarin kayayyakin tarihi na kasashe daban daban, sun halarci bikin sake bude ma'adanar. A wajen bikin, Muhammad Ahmad, ministan al'adu na kasar Syria, ya bayyana cewa, cikin ma'adanar kayayyakin tarihin an ajiye shaidu game da sakamakon da aka samu bisa raya al'umma da al'adu a kasar Syria, saboda haka ma'aikatar al'adu ta kasar zata ci gaba da kokarin kare kayayyakin tarihin, da ganowa da kuma nazarinsu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China