in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci liyafar da sarki Felipe na VI na kasar Spaniya ya shirya
2018-11-29 10:18:59 cri

Jiya da dare ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping dake ziyara a kasar Spaniya ya halarci liyafar da sarki Felipe na 6 na Spaniya ya shirya a fadarsa dake birnin Madrid don yi masa maraba da zuwa kasar Spaniya.

Sarkin ya bayyana cewa, kasashen biyu na mu'amala sosai a a fannoni daban daban, bangarorin biyu sun goyon bayan ra'ayin bangarori daban daban da yin ciniki cikin 'yanci, kana suna da ra'ayi iri daya kan batutuwan tinkarar sauyin yanayi da nuna goyon baya ga bunkasuwar kasashen Afirka da dai sauransu.

A nasa jawabin, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana son hada kai tare da kasar Spaniya don samar da kyakkyawar makoma ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a sabon zamani. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China