in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da sarkin kasar Felipe VI na Spaniya
2018-11-28 11:19:03 cri
A jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sarki Felipe na 6 na kasar Spaniya a fadar Zarzuela dake birnin Madrid na kasar ta Spaniya.

Xi Jinping ya bayyana cewa, yana farin ciki da wannan ziyara da ya kawo kasar Spaniya bisa gayyatar da sarki Felipe ya yi masa. Ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kasar Spaniya ita ce ta farko da ya kai ziyara nahiyar Turai tun bayan da ya ci gaba da zama shugaban kasar Sin, kana ita ce zango na farko a ziyarar da yake a nahiyar Turai da Latin Amurka a wannan karo.

Ya ce, yana fatan ziyarar za ta kara sada zumunta da inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin tana farin ciki da ganin ci gaba da raya nahiyar Turai bisa tsarin bai daya, kana yana fatan kasar Spaniya za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da kasashen Turai.

A nasa bangare, sarki Felipe ya bayyana cewa, tun bayan da Spaniya da Sin suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu sun girmama tare da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan da suke shafar muradunsu. Kasar Spaniya tana son ci gaba da yin mu'amala tare da kasar Sin don kara yin hadin gwiwa a bangarori daban daban da kara zurfafa dangantakar dake tsakanin Turai da kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China