in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Spaniya sun yi alkawarin zurfafa alakar dake tsakaninsu
2018-11-29 09:20:55 cri

A wani labarin kuma, kasashen Sin da Spaniya sun yi alkawarin zurfafa alakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a sabon zamanin da ake ciki. Sin kuma amince su kiyaye dokokin kasancewar bangarori daban-daban da inganta alaka a fannoni daban-daban.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka rabawa manema labarai, yayin ziyarar aikin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai kasar ta Spaniya. Alakar kasashen biyu dai tana kunshe da sabbin damammaki na raya kasa, yayin da a wannan shekarar kasashen biyu ke cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu, matakin da zai kara taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba da ma kyakkyawar makoma a duniya.

Sanarwar ta bayyana cewa, bangaren Spaniya ya sake nanata cewa, zai martaba manufar kasar daya tak a duniya. Kasar Spaniya dai ita ce zangon farko na ziyarar da shugaba Xi ke yi a Turai da Latin Amurka, ziyarar da za ta kai shi kasashen Argentina da Panama da kuma Portugal.

Shugaba Xi zai kuma halarci taron kolin kungiyar G20 karo na 13 da zai gudana a birnin Buenos Aires na kasar Argentina.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China