in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Spaniya sun amince su zurfafa alakar dake tsakaninsu
2018-11-29 09:05:05 cri

A jiya ne kasashen Sin da Spaniya suka amince su kara zurfafa alakar shekaru 45 da kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu, ta yadda al'ummomin kasashen biyu za su kara cin jin gajiyar wannan dangantaka.

Kasashen biyu sun cimma wannan matsaya ce, yayin wata ganawa tsakanin Firaministan kasar Spaniya Pedro Sanchez da shugaba Xi Jinping na kasar Sin dake ziyara a kasar ta Spaniya a halin yanzu.

A jawabinsa shugaba Xi ya ce, kasarsa na son hada kai da Spaniya don kara yaukaka alakar sassan biyu bisa manyan tsare-tsare, da daga matsayin alakarsu a fannonin daban-daban zuwa gaba, don zama abin misali, ta yadda zuriyoyin dake tafe za su yi koyi da juna, da ma yadda kasashe masu mabanbantan tsarin zamantakewa za su amfana da alakar moriyar juna.

A nasa jawabin, firaminista Pedro Sanchez na Spaniya, ya bayyana cewa, kasarsa na goyon bayan tsarin kasancewar bangarori daban-daban, da ma matsayin kasar Sin game da harkokin kasa da kasa. Ya kuma bayyana kudurinsa na ci gaba da tattaunawa da kasar Sin don inganta kyakkyawar alaka tsakanin Turai da kasar Sin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China