Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, Sin da Spaniya suna cikin muhimmin lokacin yin kwaskwarima da samun bunkasuwa, don haka zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da sada zumunta da fadada hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare sun dace da muradun kasashen biyu da jama'arsu, kana sun taimaka wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun wadata a duniya baki daya.
Bayan ya gama ziyara a kasar Spaniya, shugaba Xi Jinping zai kai ziyara kasashen Argentina da Panama da Portugal, tare da halartar taron koli na kungiyar G20 karo na 13 da za a gudanar a birnin Buenos Aires dake kasar Argentina. (Zainab)