Kasar Sin na son cimma matsaya tare da sauran bangarori wajen taron G20
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya furta a yau Laraba a birnin Beijing na kasar Sin cewa, kasar Sin na fatan ganin taron kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na G20 ya yi amfani, wajen taimakawa tattalin arzikin duniya, ta yadda zai bi hanyar ci gaba mai dorewa da daidaito. Sa'an nan kasar Sin za ta yi kokari tare da sauran bangarorin duniya, don neman cimma matsaya a wajen taron. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku