in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan ganin an cimma matsaya tsakanin kungiyar EU da Birtaniya
2018-11-26 20:49:55 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya furta a yau Litinin cewa, kasar Sin na mai da cikakken hankali kan batun ballewar kasar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai EU, haka kuma kasar na fatan ganin Birtaniya da EU sun cimma matsaya a karshe.

Wani labarin da aka ruwaito ya ce, kungiyar EU ta zartas da yarjejeniyar ballewar kasar Birtaniya daga EU, da wata sanarwa mai alaka da huldar dake tsakanin Birtaniya da EU a nan gaba, duk a jiya Lahadi.

Dangane da batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, kungiyar EU da kasar Birtaniya dukkansu abokan kasar Sin ne, wadanda ke hadin gwiwa da ita bisa wasu manyan tsare-tsare. Ana son ganin nahiyar Turai da kasar Birtaniya sun zama masu walwala, da zaman lafiya, tare da bude kofofinsu ga kasashen waje, kasancewar hakan zai amfani kowa da kowa. Don haka kasar Sin na fatan ganin bangarorin 2 sun cimma matsaya a karshe. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China