in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Ba za a samu nasarar lalata zumuncin Sin da Pakistan ba
2018-11-27 19:13:46 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya furta a yau Talata cewa, duk wani yunkuri na lalata zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Pakistan ba zai yi nasara ba. Ya ce kasar Sin ta yi imanin cewa, Pakistan za ta iya tabbatar da kwanciyar hankali a cikin gidanta, tare da daukar kwararan matakai wajen ba da kariya ga Sinawa, da kamfanonin kasar Sin dake kasar Pakistan.

Wata sanarwar da bangaren Pakistan ya gabatar ta nuna cewa, harin da aka kai wa ofishin karamin jakadan kasar Sin dake Karachi a ranar 23 ga watan da muke ciki, hari ne na ta'addanci, lamarin da ya haddasa mutuwar masu gadi 2. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China