in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai ziyarci kasashen Spaniya da Argentina da Panama da Portugal tare da halartar taron kungiyar G20
2018-11-23 10:14:25 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyara Spaniya da Argentina da Panama da Portugal daga ranar 27 ga watan nan zuwa 5 ga watan Disamba, tare kuma da halartar taro karo na 13 na kungiyar G20, daga ranar 30 ga wata, zuwa 1 ga watan Decemba a birnin Buenos Aires na Argentina.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang, da ya ba da sanarwar, ya ce Shugaba Xi zai kai ziyarar ne bisa gayyatar da Sarkin Spaniya Felipe na 6 da shugaban Argentina Mauricio Macri da shugaban Panama Juan Carlos Varela da shugaban Portugal Marcelo Rebelo de Sousa suka yi masa. Haka zalika, shugaban Argentina Mauricio Macri ne ya gayyace shi zuwa taron kungiyar G20. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China