in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ci gaban kasar Sin ba ta barazana ga wata kasa
2018-11-01 10:34:49 cri
Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma Ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya ce ci gaban kasar ba za ta zama barazana ga wata kasa ba.

Wang Yi ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana bayan ganawarsa da Ministan harkokin waje da cinikayya na kasar Papua New Guinea, Rimbink Pato.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Wang Yi ya ce ci gaban kasar Sin abu ne da ya haifar da ci gaban bil adama, la'akari da yadda mutane kusan biliyan 1.4 suka fita daga kangin talauci tare da bin tafarkin wayewa, wanda ya kasance babbar gudunmuwa ga dukkan bil adama.

Har ila yau, ya ce ci gaban kasar Sin na taka rawa gaya ga wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Haka zalika, ya ce wani muhimmin bangare ne ga daukacin ci gaban dukkan kasashe masu tasowa, kuma kowacce kasa a duniya na da 'yanci samun ci gaba.

Duk wani yunkurin dakatarwa ko dankwafe 'yanci kasashe masu tasowa na neman ci gaban kansu, rashin adalci ne mafi muni da ba a taba gani ba, kuma zai zama abun kunya a tarihin duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China