in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron kwamitin sulhun MDD kan kiyaye zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa
2018-09-27 10:34:36 cri
A jiya ranar 26 ga wata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron kwamitin sulhun MDD game da wanzar da zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa a cibiyar MDD dake birnin New York.

A gun taron, Wang Yi ya bayyana cewa, kiyaye zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, muhimmin alhaki ne da ya rataya a yuwan kwamitin sulhun MDD bisa kundin tsarin mulkin majalissar, don haka ya kamata dukkan membobin kwamitin su kiyaye shi.

Game da batun hana yaduwar makaman nukiliya Wang Yi ya bayyana cewa, ya kamata a bi ka'idojin daidaita batun bisa dokoki, da kyautata tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na duniya. Kana a dauki matakai don sa kaimi ga aiwatar da aikin. Haka zalika kuma, a sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, don inganta karfin kasa da kasa na hana yaduwar makaman nukiliya, da samun zaman lafiya a duniya gaba daya.

Wang Yi ya bayyana cewa, cimma yarjejeniyar nukiliya ta kasar Iran a dukkan fannoni, na da wuyar samu a tsakanin bangarori daban daban, kuma kwamitin sulhun MDD ya amince da hakan. Ya ce Sin tana fatan kasar Iran za ta ci gaba da cika alkawarinta, kana ya kamata a girmama hakkin yin hadin gwiwar tattalin arziki, da cinikayya a tsakanin bangarori daban daban da kasar Iran.

Wang Yi ya kara da cewa, ana samun sassauci kan halin da ake ciki a zirin Koriya, kuma kasar Sin ta yi kokari kan batun. Ya ce kamata ya yi bangarori daban daban da abin ya shafa, su cika alkawarinsu na cimma burin neman samun zaman lafiya mai dorewa a zirin Koriya cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China