in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO: kiwon albarkatun ruwa zai samar da abinci a Afirka
2018-11-28 09:52:09 cri

Darektan sashen kiwon kifi da nau'o'in albarkatun ruwa na hukumar abinci da aikin gona ta MDD ko FAO Manuel Barange, ya bayyana cewa, kiwon kifi da na'u'o'in albarkatun ruwa zai taimaka wajen kawar da yunwa da karanci abinci mai gina jiki a nahiyar Afirka, ganin yadda ake fama da kamfon amfani gona sakamakon matsalar sauyin yanayi da raguwar filayen noma.

Manuel ya bayyana hakan ne yayin taron kolin inganta albarkatun ruwa dake gudana yanzu haka a birnin Nairobin kasar Kenya. Ya ce idan har aka samar wa kananan manoman nahiyar abubuwan da ake bukata na kiwon kifaye, hakan zai taimaka wajen samar da abinci baya ga karin kudade shiga da manoman za su samu.

Sai dai jami'in ya ce, wajibi ne a kara samar da managartan manufofi da ababan more rayuwa, muddin ana fatan cimma nasarar hakan.

Barange ya kara da cewa, kiwon kifi da ragowar nau'I'on albarkatun ruwa, wani bangaren tattalin arzikin albarkatun ruwa ne mai sarkakiya, kuma ci gabansa zai taimaka wajen samar da abinci da ma kyakkyawar makoma a nahiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China