Matia Kasaija, ministan kudi da bunkasa tattalin arzikin kasar ne ya rattaba hannun kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin Uganda yace aikin wanda zai lashe kudi kimanin dala miliyan 15 zai taimaka wajen habaka hanyoyin samun kudaden shigar kasar.
Kasaija yace, kasar Sin zata samar da na'urorin bincika jikin dan adam, da tsarin kiyaye hadura a tsarin kwastam na zamani, da abubuwan da zasu tallafawa ayyukan kwastam da dai sauransu.
Yace bayan aiwatar da ayyukan, ba za'a taba samun damar yin fasakwaurin kayayyaki ba akan iyakokin kasar.
Zheng Zhuqiang, jakadan kasar Sin a Uganda wanda ya rattaba hannu a madadin gwamnatin Sin yace, aikin wani bangare ne na tabbatar da nasarorin yarjejeniyar dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika.