Mr. Guterres ya yi kiran ne a jiya Talata, yayin zaman kwamitin tsaron MDD. Ya ce dalilan da suke haddada tashe tashen hankula a nahiyar Afirka sun hada da talauci, da rashin ayyukan yi tsakanin matasa, da tasirin sauyin yanayi, da takara wajen cin gajiyar albarkatu, da laifuka na kasa da kasa, wadanda dukkanin su ke barazana ga tsaron kasa da kasa.
A don haka ne jami'in ya bayyana cewa, kyautata ayyukan wanzar da zaman lafiya a Afirka, nauyi ne da ya rataya a wuyan daukacin sassan duniya.
Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, ya kamata duniya ta san irin tarin nauyi da ke wuyan jami'an MDD masu aikin wanzar da zaman lafiya. Kaza lika a cewar sa, MDD na fuskantar kalubale da dama, a fannin ayyukan yaki da 'yan ta'adda, wanda dole ne sai ta yi hadin gwiwa da abokan huldar ta irin su kungiyar AU da makamantan ta, kafin ta kai ga cimma nasarar shawo kan matsalolin.
Don haka dai Mr. Guterres na ganin cewa, akwai bukatar ba da gudummawa ga kungiyoyin nahiyar Afirka daban daban, ciki hadda kungiyar kasashen yankin Sahel su 5, dake yaki da ta'addanci. (Saminu)