Emelang Leteane ya ce tuni kasashen Afirka 32, suka sanya hannu kan yarjejeniyar da ta shafi baiwa al'ummun Afirka damar zirga zirga maras shinge tsakanin kasashen juna, da zama a kasashen, kamar dai yadda kungiyar hadin kan nahiyar ta AU ta bukata. To sai dai kuma akwai bukatar kasashen su tabbatar da amincewar su da yarjejeniyar kafin ta fara aiki.
Jami'in ya ce rashin maida hankali, da karancin kwarewa wajen aiwatar da manufofi irin wadannan, da ake rattabawa hannu a mataki na ministoci masu wakiltar kasashen nahiyar, ya haifar da koma baya ga yarjejeniyar.
Mr. Leteane ya bayyana hakan ne yayin taron kwamitin kwararru na UNECA karo na 22 a birnin Kigalin kasar Rwanda, wanda ya tattara wakilai daga gwamnatocin kasashen yankin gabashin Afirka. (Saminu)