in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Kamaru sun kashe 'yan aware 4 bayan mutuwar wani dan mishan Amurka a yankin da ake magana da Turancin Ingislishi
2018-11-01 13:42:18 cri
Ministan tsaron Kamaru Joseph Beti Assomo ya sanar a jiya Laraba cewa, dakarun tsaron gwamnati sun hallaka 'yan aware 4 a ranar Talata bayan mutuwar wani dan mishan kasar Amurka a Bambui, wani kauye dake shiyyar arewa maso yammacin kasar, daya daga cikin yankunan kasar biyu masu fama da rikici wanda ake magana da yaren Turancin Ingilishi a kasar.

A ranar Talata, mayakan 'yan awaren sun zargi dakarun gwamnati da hallaka dan mishan wanzar da tsaro na Amurka yayin wata musayar wuta, sai dai wani jami'in tsaron gwamnati Assomo, ya musanta zargin, ya nanata cewa 'yan awaren ne suka hallaka dan mishan wanda ya bayyana su da cewar 'yan ta'adda ne.

A cewar Assomo, 'yan awaren sun kashe Wesco a lokacin da suke kan hanyarsu ta kaddamar da hari a sansanin jami'an tsaro na Bambili da kuma jami'ar Bamenda.

Assomo yace an jikkata wani kanal din soja da wani dalibi.

Fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnati da mayakan 'yan awaren na Ambazoniya ya yi sanadiyyar raba mutane sama da 200,000 dake gudun hijira a cikin kasar ta Kamaru, kamar yadda MDD ta tabbatar da hakan.

Sama da dakarun tsaron gwamnati 150 ne aka kashe a rikicin, kamar yadda rundunar sojojin Kamarun ta sanar.

Rikicin ya kaure ne tun a watan Oktoban shekarar 2017, tun bayan da mayakan 'yan awaren suka ayyana ballewarsu daga kasar Kamaru, inda suka yi ikirarin kafa wata kasa mai suna "Ambazonia" a yankuna biyu na kasar dake magana da yaren Turancin Ingilishi a arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar Kamaru. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China