in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin dake WTO ya karyata zargin da Amurka ta yi wa salon tattalin arzikin kasarsa
2018-07-28 17:07:15 cri
A kwanakin baya, yayin taron babbar majalisar hukumar kasuwanci ta duniya ko kuma WTO a takaice, zaunannen wakilin kasar Sin dake hukumar, Zhang Xiangchen, ya musunta zargin da kasar Amurka ta yi wa salon tattalin arzikin kasar Sin.

Mista Zhang ya bayyana cewa, cikin jawabin da wakilin Amurka ya gabatar, ya ce salon tattalin arzikin kasar Sin ba irin na kasuwanci ba ne, amma idan aka dubi ka'idojin hukumar WTO, ba za'a iya gano ainihin ma'anar "tattalin arziki irin na kasuwanci" ba, kana babu wani ma'auni na "tattalin arziki irin na kasuwanci" guda daya tilo da ya dace da kowace kasa a duniya. Ya ce a halin yanzu, WTO na fuskantar kalubalen da ba'a taba ganin irinsa ba a tarihi, kuma wasu matakan da Amurka ta dauka, ciki har da takaita shigar da karafa da sanholo kasar bisa hujjar tsaron kasa, gami da kara sanya harajin kwastam bisa dokokin kanta, ita ce babbar illar dake kara ta'azzara al'amura.

Zhang ya nuna cewa, kasar Sin na son taka rawarta da bada gudummawa a fannin nazarin yadda tsarin gudanar da cinikayya dake kunshe da bangarori daban-daban ya dace da dunkulewar duniya baki daya. Amma abun dake gaban komai cikin ayyukan WTO shi ne, haramta yaduwar matakan bada kariya ga harkokin cinikayya a duniya, da lalubo bakin zaren daidaita takaddama, da kawo karshen yakin cinikayya ba tare da bata lokaci ba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China