Wasu takardun bayanai da aka wallafa, aka kuma rabawa daukacin mambobin kungiyar ta WTO a ranar Talata, sun nuna cewa Sin na bukatar sashen warware takaddama na kungiyar ko DSB a takaice, ya kau da kai game da wasu ka'idojin haramci dake kan dukkanin mambobi, ta yadda hakan zai baiwa Sin din damar zartas da wannan sabon haraji kan Amurka, duba da yadda Amurkan ta ki martaba umarnin sashen DSB.
A shekarar 2016, WTO ta baiwa Sin gaskiya game da takaddamar ta da Amurka, kan harkokin da suka shafi jibge hajoji masu arha da Amurkan ta zargi Sin da aikatawa. Kaza lika daga baya, aka sake tabbatar da wannan hukunci a dai shekarar ta 2016. To sai dai kuma Sin ta yi korafin cewa, ba wani kwakkwaran mataki da Amurkan ta dauka, na aiwatar da wannan hukunci yadda ya kamata.
Idan har wannan bukata ta Sin ta tabbata, za ta samu damar karawa hajojin da take shigarwa Amurkan harajin da ya kai dala biliyan 7.043 a ko wace shekara. (Saminu Alhassan)