in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagororin Afirka na nazarin hanyoyin kare ikon mallakar fasahohi domin bunkasa kirkire kirkire
2018-11-20 09:38:12 cri
Mataimakiyar minista a ma'aikatar inganta masana'antu, cinikayya da raya sana'o'i ta kasar Namibia Lucia Ipumbu, ta ce shugabannin Afirka sun sha alwashin aiwatar da matakai, wadanda za su bunkasa kirkire kirkire, da kare ikon mallakar fasaha a daukacin nahiyar.

Ipumbu ta bayyana hakan ne yayin taro na 42, na mambobin kwamitin zartaswa dandalin ARIPO, wanda ke da nauyin kare ikon mallakar fasahohi a Afirka.

Uwar gida Ipumbu, ta ce kare ikon mallakar fasaha, na baiwa masu sana'o'in kirkire kirkire kwarin gwiwar bunkasa tattalin arziki, da samar da kyakkyawan muhalli na gogayyar cinikayya.

Yayin taron na birnin Windhoek, ana sa ran mahalartan sa za su nazarci hanyoyin magance kalubalen da al'ummar nahiyar ke fuskanta, game da kare ikon mallakar fasaha.

ARIPO hukuma ce ta kasa da kasa dake samar da damar hadin gwiwa wajen cudanya a fannin kariya ga ikon mallakar fasaha, da cudanya tsakanin masu ruwa da tsaki. A bana taron na birnin Windhoek ya samu mahalarta daga kasashe 19, zai kuma gudana tsakanin ranekun 19 zuwa 23 ga watan nan na Nuwamba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China