Jami'ar babban bankin duniya mai lura da harkokin raya ilimi a gabashin Afirka Sajitha Bashir, ta ce ci gaban nahiyar Afirka ta fuskar tsaro da zaman lafiya, da bunkasar tattalin arziki, ya ta'allaka kacokan kan irin sauye sauye da nahiyar ta aiwatar a fannin raya ilimi.
Sajitha Bashir, ta bayyana hakan ne a jiya Alhamis, a gefen taron karawa juna sani na masu ruwa da tsaki a fannin raya ilimin nahiyar, wanda ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya. Ta ce, managarcin tsarin samar da ilimi, zai tallafawa nahiyar wajen yin takara a fannin bunkasar tattalin arziki, tare da samar da dama ta magance kalubalen zamantakewa da na siyasa da nahiyar ke fama da su.
Mahalarta taron dai sun hada da ministocin ilimi na kasashen Afirka, da masu tsara manufofi, da wakilan manyan hukumomin kasa da kasa, da masu rajin bunkasa ilimi. Dukkanin sassan dai sun amince da muhimmancin dake tattare da bunkasa ilimi, a matsayin hanyar fadada ci gaban nahiyar baki daya.(Saminu)