Wani kwararre a fannin ci gaban ilimi dake aiki karkashin kungiyar hadin kan Afirka ta AU Callistus Ogol, ya yi kira ga gwamnatocin Afirka, da su fadada zuba jari a fannin samar da fasahohin amfani da yanar gizo masu inganci domin raya ilimi.
Callistus Ogol, ya yi wannan kira ne a jiya Laraba, yayin wani taron karawa juna sani game da bunkasa sha'anin ilimi a nahiyar, wanda ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya.
Callistus Ogol, ya ce fasashonin zamani na yada bayanai, za su karfafa kokarin da ake yi, na rage al'ummun nahiyar da ba sa iya karatu da rubutu, kasancewar Afirka nahiya ta biyu a girma a dukkanin duniya.
Jami'in ya kara da cewa, nahiyar Afirka na iya cin muhimmiyar gajiya daga harkokin zuba jari a fannin amfani da yanar gizo mai sauri, wadda za ta taimaka wajen samar da ilimi a dukkanin sassan Afirka, ciki hadda lunguna da sakon nahiyar.
Ministoci da masu ruwa da tsaki wajen tsara dokoki, da masana, sun halarci taron na yini uku, sun kuma amince da cewa, fasahar sadarwa na sahun gaba wajen kara inganta harkar koyo da koyarwa, da ma batun horas da matasa sana'o'i.(Saminu)