in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun bukaci a mayar da tsarin koyarwa ta hanyar fasahohin zamani a Afrika
2018-09-28 10:17:56 cri
Masana harkokin tattalin arziki na nahiyar Afrika sun bukaci a bunkasa tsarin karantarwa ta hanyar fasahohin zamani a fadin nahiyar domin cimma nasarar sauya fasalin ilmi a tsakanin al'umma.

A jawaban da suka gabatar a lokacin taron kasa da kasa karo na 13 na baje kolin ilmin fasahar sadarwa ta zamani ICT, da ba da horo, da samar da kwarewa a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

Suleiman Adamu, shugaban sashen ilmin fasahar sadarwa ta zamani na jami'ar Sule Lamido dake Najeriya, ya nanata cewa, ilmin fasahohin zamani zai tabbatar da ci gaban ajandar nan ta bunaksa ci gaban gwamnatocin kasashen Afrika, da hukumomi masu zaman kansu har ma da fannin kungiyoyin fararen hula a matsayin wani yunkuri na sauya fasalin tsarin ilmin al'umma.

Kasashen Afrika suna bukatar kwarewar ilmi domin su samu damar gudanar da ayyuka, da koyarwa da kyautata hanyoyin sadarwa ta hanyar amfani da fasahohin zamani domin kaucewa zama saniyar ware a tsarin harkokin duniya, in ji Ebenezer Malcalm, shugaban sashen ilmin mai zurfi na jami'ar kimiyya da fasaha ta kasar Ghana (GTUC).

Taron ya samu halartar masana da masu tsara dabarun shugabanci sama da 1,000 daga bangarorin ilmi da harkokin cinikayya na kasashen Afrika da sauran sassan duniya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China