in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin kasashen Afirka za su yi taro a Kenya game da muradun ci gaba mai dorewa
2018-04-18 20:17:47 cri
Ministocin ilimi na kasashen Afirka za su gudanar da wani taro na yini uku tsakanin ranekun 25 zuwa 27 ga watan nan a birnin Nairobin kasar Kenya, domin tattauna batutuwan da suka shafi kudurin cimma muradun ci gaba mai dorewa a fannin ilimi.

Taron wanda za a bude cikin mako mai zuwa, zai nazarci halin da ake ciki game da wadannan muradu na SDGs. Zai kuma gudana ne karkashin inuwar hukumar UNESCO ta MDD, da kuma kungiyar hadin kan Afirka ta AU. Kaza lika zai tara ministoci, da masu ruwa da tsaki wajen tsara manufofin ilimi, da masu fada a ji a fannin ilimi daga tsagin gwamnatoci da sassa masu zaman kan su.

Ofishin hukumar UNESCO ya bayyana cewa, mahalarta taron za su tattauna da nufin kara fahimta, da musayar ra'ayoyi game da hanyoyin daidaita manufofin SDG4 na raya ilimi, da kuma wanda nahiyar ke da shi karkashin shirin CESA. Ta yadda manufofin za su tallafawa tsarin da ake da shi na dokokin raya ilimi, da manufofin cimma nasarar hakan, tare da tsare tsaren samar da kudade, da sanya ido, tare da tattara bayanai masu nasaba da hakan.

Ana hasashen cewa, yayin taron na wannan karo, ministocin za su yi kokarin cimma matsaya guda ta samun ci gaba, wadda za ta bada damar samar da ilimi mai nagarta ga daukacin al'ummun nahiyar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China