in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da yiwa dakarun C-VEO gyaran fuska
2018-11-16 11:59:29 cri
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da yiwa ma'aikatan hukumar yaki da ayyukan ta'addanci(C-VEO) dake aiki a rundunar hadin gwiwar Amurka da Afirka (AFRICOM) gyaran fuska.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a jiya Alhamis na cewa, nan da wasu shekaru masu zuwa za a rage kasa da kaso 10 cikin 100 na ayyukan hukumar mai sojoji 7,200 dake aiki a rundunar dake Afirka .

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ayyukan da hukumar yaki da ta'addanci take gudanarwa a kasashen Somliya, da Djibouti da Libya ba za su canja ba, sai dai kuma za a canja fasalin ayyukan da take gudanarwa a wasu yankuna, kamar yammacin Afirka, daga taimakon dabaru zuwa na ba da shawara, hada kai da musayar bayanan sirri.

Manufar ayyukan dakarun dai ita ce, kare galibin alakar hadin gwiwa da shirye-shiryen tsaron Amurka a Afirka domin karfafa alakar hanyoyin samun bayanai, da kara karfin kawance da taimakawa shiryen-shiryen da ake gudanarwa.

Ma'aikatar tsaron ta kara da cewa, manufar yin gyaran fuskar ita ce taimakawa muhimman matakan da aka zayyana a manufofin tsaron kasar ta Amurka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China