in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Amurka: Babu wani shamaki game da yin huldar bankin da Sudan
2018-04-30 15:56:11 cri
Mataimakin sakataren Baitul malin Amurka Marshall Billingslea ya bayyana cewa, babu wani shinge game da yin mu'amalar harkokin banki da kasar Sudan, bayan da Amurkar ta dagewa kasar takunkumin da ta kakaba mata.

Jami'in na Amurka wanda ya bayyana hakan bayan zantawa da jami'an kasar Sudan yayin ziyarar da ya kai Khartoum a jiya Lahadi, ya kuma yi alkawarin dawo da hadin gwiwa tsakanin bankunan Amurka da na Sudan.

Ya ce, Sudan ta samu ci gaba a shirye-shirye guda biyar da aka tsara mata, abin da ya sa aka dage mata takunkumin tattalin arzikin da aka sanya mata. Haka kuma majalisar dokokin Amurkar na duba yiwuwar fitar da sunan Sudan cikin jerin sunayen kasashen dake goyon bayan ayyukan ta'addanci.

A ranar 6 ga watan Oktoba ne, Amurka ta yanke shawarar dagewa Sudan takunkumin tattalin arzikin da ta kakaba mata baki daya, inda ya ba da misali da kwararan matakan da Sudan ta dauka na tsagaita bude wuta a yankunan da ake fama da tashin hankali a kasar, da inganta yanayin kai kayan agaji a fadin kasar, da hada kai da Amurka wajen magance rikice-rikicen da ake fama da shi a yankin da ma barazanar ta'addanci.

Koda yake har yanzu Sudan ba ta fita daga jerin kasashen da Amurka ke dauka a matsayin masu taimakawa 'yan ta'adda ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China